Wasu Daga Cikin Dalilin Da Yasa Nzeogwu Ya Kashe Sardauna

YADDA MUKA YI DA NZEOGWU BAYAN YA KASHE SARDAUNA – MARIGAYI SHEIKH ABUBAKAR GUMI

Kamar karfe hudu na asuba ranar juma’a aka bugo min waya bayan na dauka sai naji ministan ilimi na Arewa Alhaji Isa Kaita. Ya ce min sojoji sun yi Juyin mulki, har an kai wa gidan Sardauna hari kamar yadda ya ce min duk manyan jami’an gwamnati sun buya. Ya ce min ya yi magana da Hassan Katsina, amma Hassan a lokacin ya ce mai babu abin da zai iya yi.

Hassan ya ce mai a wannan lokacin ma yana ganawa ne da bujirarrun sojojin. Isa Kaita, ya ce min ya kamata ni in tafi gidan Sardauna in gani idanuwa na abin da ke faruwa.

Bayan na kintsa nayi sallar subahi, na kuma kama hanya na nufi gidan Sardauna, naje na ishe gidan anyi kacha-kacha da shi alamu kuma sun nuna anyi amfani da manyan makamai wurin lalata gidan. Har lokacin da na isa gidan hayaki ne a turnuke. Sai wasu tsirarun sojoji a tsaye da bindigogi a hannun su, ko ina tsit. Haka na wuce su na kutsa kai cikin gidan, ina shiga naci karo da gawar Sardauna a kwance a filin da ake ajiya motoci na gidan.

Nan da nan na ce a dauki gawar a kai ta gidan, Sarkin Musulmi, da ke unguwar Sarki. Sardauna, da shi da uwargidan shu Hafsat aka kashe su.

Bayan mun gama shirya shi, rana kuma ta fara dagowa nine na sallaci duka gawarwakin. Ina sane kuma da cewa anyi babban rashi, kuma nan kurkusa abu ne mawuyaci a samu kamar shi.

Akan hanya ta, ta dawowa gida daga wurin jana’izar Sadauna, na wuce gun-gun mutane sun taru suna ta alhinin abin da ya faru. Bayan na samu natsuwa abubuwa sun koma kamar yadda suke ranar komawa aiki na shirya kamar kullun na tafi wurin aiki na. Ina cikin ofishi na da safe sai ga motar sojoji, shake da sojoji, ta shigo harabar wurin aiki na. Wasu daga cikin sojojin suka sauko a mota suka tambayi inda ofishi na yake. Bayan sun shigo ofishi na sukai min gaisuwa irin ta ta girmamawa, suka ce an turo su tafi da ni maigidan su Nzeogwu, yana son gani na.

Kuma zan shiga motar su ne tilas su tafi da ni amma zan iya sa wani cikin ma’aikata na ya bi mu a baya shi sai ya dawo da ni. Na tashi na bisu ban yi musu ba na umarci direba na ya bi ni da mota bayan mun gama ganawa ya dawo da ni. Bayan mun isa barikin sojan inda shi Nzeogwu yake. Naga sojoji da yawa suna gadin barikin kowane soja sabe yake da bindigar shi.

Bayan mun yi fakin muka sauko daga mota muka shiga cikin ofishin, cikin mu ba wanda yai ma wani magana tsakani na da wadannan sojojin. Bayan sun kai ni inda Nzeogwu, yake, ya kuma tare ni cikin fara’ar shi na kuma zauna akan kujera, sai ya fara magana cikin tattausar murya.

Abunda yake son sani shine ina muka boye makaman da muka siyo? Wannan tambayar tasa tabani matukar mamaki, naga nide a rayuwata banma taba ganin Nzeogwu ba, ban Kuma taba wata alakar ta rayuwa dashi ba. Ni a tunanima shi ne ya kirani yaimun ta’aziyar rashin Sardauna, dana yi kokuma ya nuna dana saninsa akan abunda ya aikata. Dama ban yi tsammanin kalamai na banhakuri daga gareshi ko nadama akan abunda ya aikata tunda na lura yana al’afari da abunda ya aikata.

Abunda Kuma ya kara bani mamaki Wanda suka sabi makamai sukayi Juyin mulki wai a lokacinne suke kokarin tattara hujjojinsu ko kuma dalilan hambarar da wannan gwamnatin.

Sai na gama kafin in bashi amsar tambayarsa ya kamata in nemi karin bayani daga gare shi. Sai ya ce mun a irin labaran daya samu an cemai mun siyo makamai masu tarin yawa mun shigo da su cikin kasa, Kuma mun siyo makaman ne daga kasashen gabas ta tsakiya. Kuma niyarmu itace mu kaddamar da jahadi akan wayanda ba musulmi ba, shiyasa ya ke so in gayamai inda muka boye makaman.

Lokacin da na zo ba shi amsar tambayarsa na tabbatar mai cewar ni a wurinsa ma na farajin wannan maganar, na Kuma tabbatar Ina magana ne a matsayina na mashawarcin Sardauna, akan harkokin da suka shafi addinin Musulunci. Kuma na tabbatar mai da cewa Sardauna, bai taba zuwa wata kasar larabawa a matsayinsa na firimiya ba tare da daniba. Kuma bantaba ji yai maganan makamai ba a wata kasar larabawa, ballema har musiyo mu shigo dasu Najeriya, da sunan wai zamu yaki wayanda ba musulmaiba.