WASSCE Ta bayyana Ranar Da Za’a Fara Rubuta Jarabawar 2022

Hukumar Shirya Jarrabawar Afirka ta Yamma, West African Examination Council (WAEC) ta bayyana ranar da za’a fara rubuta jarrabawar shekarar 2022.

WAEC ta ce WASSCE za ta fara aiki ne a ranar Litinin 16 ga Mayu, 2022.

Da yake magana a wani taron tattaunawa a ranar Litinin, shugaban ofishin WAEC na kasa, Mista Patrick Areghan ya lura cewa jarrabawar za ta ƙare a ranar 23 ga Yuni 2022.