Al'umma

Waɗanda Ba Su Yarda Da Auren Mace Fiye Da Ɗaya Ba Suna Taimakawa Karuwanci – Munir

Wani lauya kuma dan siyasa a Najeriya, Prince Chinedu Munir Nwoko, wanda aka fi sani da Ned Nwoko, ya zargi mazan da ba su auri fiye da mace daya ba da haddasa lalata a cikin al’umma.

Tsohon dan majalisar wanda ya bayyana hakan a wata hira da yayi da jaridar Guardian a kwanakin baya, ya bukaci mazan Najeriya da su yi koyi da mazan arewa ta hanyar auren mata fiye da daya.

Yace: “Mata da yawa suna wajen ba su da miji, musamman a yankin kudancin kasar nan, kuma ana yawan karuwanci. Idan mutanen kudu suka yi koyi da takwarorin su na arewa ta hanyar auren mata fiye da daya, watakila hakan zai iya canja lamarin.

“Matsakaicin dan kudu yana iya samun mace daya tare da budurwai, kuma yana kashe wa budurwa kudi, wani lokacin ma fiye da matar shi.

“Misali, mutumin da yake da mata uku, yana mai da hankali a kan su, duk kuɗin da ya samu yana kashewa ga iyalin shi, kuma yana yiwuwa ba ya da budurwa ko ƙwara-ƙwara. Kuɗin da waɗanda suke da ‘yan mata da yawa suke kashewa ga banza ne, ba jarin iyali ba ne.”

Nwoko, wanda ke da mata da yawa, ya lura cewa shi da Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi, suna yiwa Najeriya hidima ta hanyar auren mata da yawa.

Ned, wanda ya kara da’awar cewa suna da asali irin na Ooni, ya bayyana cewa kakannin su sarakuna ne kuma sun yiwa Najeriya hidima a wannan matsayi. “Kuma yanzu haka muna yiwa Najeriya hidima ta hanyar auren mata da yawa.”

Advertisement