Uwa Na Da Damar Auren Tsohon Saurayin Yar Ta – Hisbah Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano a ranar Talata ta yi watsi da tatsuniyoyi game da auren wata uwa da ta auri tsohon mai neman auren ‘yar ta a karamar hukumar Rano ta jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa matar mai suna Malama Khadija ta rabu da mijin ta inda ta auri saurayin diyar ta. Lamarin ya faru ne bayan diyar matar mai suna A’isha ta ki amincewa da wanda ke neman auren ta, lamarin da ya janyo cece-ku-ce da ya sa hukumar ta Hisbah ta kafa kwamitin da zai binciki lamarin. An mika rahoton kwamitin da ya binciki badakalar auren a ranar Talata da yamma.

Shugaban kwamatin kuma mataimakin kwamanda mai kula da ayyuka na musamman na Hisbah Hussain Ahmed ya gabatar da rahoton, inda ya bayyana cewa kwamitin ya gano cewa auren ya halatta kuma ya cika dukkan sharrudan da suka dace. Ya ce matar mai suna Khadija, tsohon mijin ta ne ya sake ta, kuma ta jira watanni uku da Musulunci ya ba ta kafin ta auri wani mutum da ‘yar tata ta ki a baya.

Ahmed ya musanta rade-radin da ake yadawa na cewa Khadijah tana haduwa da sabon mijin na ta, tana aure kuma ta tilastawa mijin ta ya sake ta domin mai neman diyar ta ya aure ta. Ya bayyana cewa auren halas ne a karkashin addinin Musulunci, dalilin da ya sa kwamandan Hisbah na karamar hukumar Rano ya amince da kuma halartar bikin aure.

Babban kwamandan hukumar ta Hisbah Sheikh Haruna Ibn Sina ya mayar da martani inda ya yabawa kwamitin kan kwazon da ya yi. Ya yi da’awar cewa an zabo ‘yan kwamitin ne cikin tsanaki saboda sanin ilimin da suke da shi a kan ka’idojin Musulunci da daidaita al’umma.