Tunawa Da Albarkar Watan Ramadan A Gaza

An shiga watan Ramadan mai alfarma. Musulmai a fadin duniya suna azumi, suna ciyarwa da samun lokaci tare da iyalan su tare da sadaukar da kan su domin addu’a da ibada. Amma su musulmin Gaza, wannan wata mai alfarma na cike da bacin rai da bakin ciki a gare su.

Sama da watanni biyar kenan suna fama da kisan kiyashi, cututtuka, yunwa da kishirwa a hannun sojojin Isra’ila. Tashin hankali da rashin tausayin su bai tsaya ko raguwa ba yayin da watan Ramadan ya fara ba.

Yayin da da yawa daga cikinsu ke ta faman neman abinci domin yin buda baki ko kuma samun wurin da za a yi sallah lafiya, abubuwan da suka rika tunawa a watan Ramadan da suka gabata suna sa su firgici.

A yayin da ake ci gaba da hargitsin jirage marasa matuka na Isra’ila da karar fashewar bama-bamai, mutane da yawa sun rufe idona suna tunawa da daukakar watan Ramadan a Gaza.