Al'umma

Tsahon Ma’aikacin Gidan Radiyon VOA Hausa, Kabiru Usman Fagge Ya Rasu

Tsohon ma’aikacin gidan rediyon VOA Hausa, Amurka, Alhaji Kabiru Usman Fagge ya rasu a a kasar Amurka bayan yayi fama da rashin a kasar, Washintan DC.

An haifi Mallam Kabiru Usman Fagge ne a jihar Kano, Najeriya a ranar 12 ga watan Satumban shekarar 1946, kimanin shekaru 77 da suka gabata.

A shekarar Mallam Fagge, a 1956 ya shiga makarantar farko, Firamare ta yankin Fagge a jihar kano, sannan kuma a shekarar 1969 ya kamala karatun gaba ga firamare. Daga bisani ya zarce zuwa Kolejin Horas da Malamai ta Bichi inda ya shekara uku a wannan fanni.

Bugu da ƙari, Usman Fagge ya kammala a Kolejin horas da malamai ta Kano, KTC a shekarar 1970, inda ya sami takardar shaidar koyarwa mai daraja ta biyu (Grade 2).

Ya bar duniya yana shekaru 77.