Al'umma
Timbuktu: Ɗaya Daga Cikin Jami’o’i Mafi Daɗewa A Duniya
Ilimin lissafi na yau (Mathematics) ya fara a can, Timbuktu a Mali ya samo asali ne a kusan 1,100 BC, lokacin da makiyaya Abzinawa suka kafa ta a matsayin sansanin yanayi.
Bugu da ƙari, wurin da yake a gefen hamada yana nufin ya zama babban birnin kasuwanci, kuma a karni na 14 ya kasance abu mai mahimmanci ga cinikayyar gishiri da zinariya.
Al’adarta ta ilimi ta samo asali ne tun lokacin da aka shigar da ita cikin daular Mali a karni na 13, inda addinin da ya mamaye yankin shi ne Musulunci, kuma an kafa masallatai da dama.