Tarihi Zai Tuna Ta’addanci Tsawon Lokaci Bayan An Shafe Isra’ila – Khamenei

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce wata rana Isra’ila za ta daina wanzuwaa ban ƙasa, amma za a tuna da ayyukan da ta yi na ta’addanci kan Falasdinawa.

“Wadannan laifuka za su kasance a tarihi. Ko bayan faduwar gwamnatin sahyoniyawan da za’a tarwatsa da kuma kawar da su daga doron kasa da taimakon Allah, ba za a manta da wadannan laifukan ta’addanci ba,” kamar yadda ya fada a wani taro a birnin Qum, na kasar Iran.

“A wannan ranar, za a rubuta a cikin littattafan tarihi cewa akwai mutanen da suka zo mulki a wannan yanki na Gabas Ta Tsakiya, kuma suka aikata laifuka masu yawa tare da kashe dubban yara da mata a cikin makonni kaɗan.”

Khamenei ya ce “wadanda suke gani a fili” sun dade suna hasashen cewa za a ci nasara a kan Isra’ila kuma Falasdinawa za su yi nasara.

Ta’addancin Isra’ila

Kungiyar kare hakkin yara ta kasa da kasa ta Defence for Children International ta ce an kashe akalla yara kanana Falasdinawa 8,000 a zirin Gaza da kuma 121 a yankin yammacin gabar kogin Jordan da kuma birnin Kudus aka kashe a shekarar 2023, inda ta kira 2023 da “shekarar kisan kiyashi” da sojojin Isra’ila suka yi.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta ce adadin kisan gillar da aka yiwa yaran Falasdinawa a hannun sojojin Isra’ila a cikin shekarar da ta gabata ba a taba ganin irinsa ba, wanda ke nuni da cewa yaran Palasdinawa ne manyan hare-haren Isra’ila.

Har ila yau, ana sa ran adadin yaran da aka kashe zai karu sosai, yayin da har yanzu dubban yara ke bacewa a Gaza, wadanda suka makale a karkashin baraguzan gidajensu da aka kai musu harin bama-bamai da ake kyautata zaton sun mutu.

Haka kuma, katse hanyoyin abinci da ruwa da wutar lantarki da magunguna da man fetur da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan asibitoci da makarantu da gidajen biredi da tashohin ruwa da filayen noma ba makawa zai haifar da mutuwar kananan yara.