Al'umma

Jihohi 10 Mafi Yawan Mutane A Najeriya

Najeriya na daya daga cikin kasashen duniya da ke da dimbin al’ummar da ke zaune a ciki. A Afirka, ita ce ke da mafi yawan al’umma kuma wannan shine daya daga cikin dalilan da ake mata lakabi da Giant Of Africa.

Najeriya tana da jihohi talatin da shida amma a wannan makala, mun tattauna jihohi goma ne kawai suka fi yawan jama’a a ƙasar.

Ga sunayen jihohin:

1. Jihar Legas: A halin yanzu, jihar Legas ita ce jiha mafi yawan jama’a a Najeriya, inda mutane miliyan 21 ke zaune a ciki. Wannan kuma ya sanya ya zama birni mafi yawan jama’a a yammacin Afirka.

2. Jihar Kano: Jihar Kano ita ce jiha ta biyu mafi yawan al’umma a Najeriya mai yawan mutane miliyan 16.

3. Jihar Oyo: Jihar Oyo ita ce jiha ta uku mafi yawan al’umma a Najeriya inda mutane miliyan 15 ke zama a ciki.

4. Jihar Kaduna: Jihar Kaduna ce ta zo ta hudu a cikin jihohi goma da suka fi yawan jama’a a Najeriya inda mutane miliyan 12 ke zaune a ciki.

5. Jihar Ribas: Jihar River dai na daya daga cikin jihohin da ke da yawan jama’a a Najeriya inda mutane miliyan 11 ke zaune a ciki.

6. Jihar Katsina: Jihar Katsina ce ta zo ta shida a cikin jihohi goma mafi yawan al’umma a Najeriya inda mutane miliyan 10 ke gudanar da ayyukan a ciki.

7. Jihar Bauchi: Jihar Bauchi kuma tana daya daga cikin jahohin Najeriya da ke da yawan jama’a da mutane miliyan 9 ke zaune a ciki.

8. Jihar Anambra: Jihar Anambra ita ce jiha ta takwas a yawan jama’a a Najeriya da mutane miliyan 8.3 ke zaune a ciki.

9. Jihar Jigawa: Jihar Jigawa na daya daga cikin jahohin da suka fi yawan al’umma a Najeriya da mutane miliyan 8 ke zaune a ciki.

10. Jihar Binuwai: Jihar Benue ita ce jiha ta goma mafi yawan al’umma a Najeriya inda mutane miliyan 7.8 ke gudanar da ayyukan a ciki.