Al'umma

Tarihin Rayuwar Murja Kunya

An haifi Murja wacce asalin sunan ta shi ne Murja Ibrahim Kunya a garin Kunya kimanin shekara 27 zuwa 28 da suka gabata a garin na Kunya.

Mahaifin Murja shi ne malam Ibrahim da mahaifiyar ta malama Hindatu, dukkanin mahaifan ta mazauna garin Kunya ne.

Sai dai Murja ba tayi karatun zamani ko daya ba, amma ta halarci wata makarantar Islamiyya ta Fodiyya da ke cikin garin Kunya.

Amma kuma, kafin Murja ta kammala makarantar Fodiyya sai mahaifanta suka cire ta daga makarantar sannan suak aurar da ita, inda ta fara auren wani da aka bayyana cewa shi ɗan sanda ne a garin Minjibir.

Haka zalika, bayan mutuwar auren na farko ta sake auren wani a karo na biyu a garin Gandurwawa duka a ƙarƙashin ƙaramar hukumar ta Minjibir dai.

A wannan karon, bayan Murja ta rabu da mijin nata na biyu ta kuma Murja ta koma garin Kunya kafin daga baya kuma ta bar mahaifarta zuwa birnin jihar Kano kimanin shekaru 10 da suka gabata.

To daga karshe bayan komar ta a Kano abubuwan da ke gudana suka biyo baya, kuma suke ci gaba da gudana.