Al'umma

Tarihin Rahama Haruna, Yarinyar Da Ta Rayu A Cikin Botikin Roba Har Ta Rasu

Rahma Haruna ‘Yar Kauyen Lahadi Makole a Jihar Kano Najeriya ce ‘yar shekara 19 da labarin ta ya shahara tunda wani hoto da mai daukar hoto Sani Maikatanga ya dauki hotunan ta ya wallafa a shafin shi na Instagram.

An haifi Rahma Haruna wani lokaci tsakanin 1996 zuwa 1997, a Birnin Kano Najeriya, tana da shekara shida Rahama kafafuwan ta da hannayen ta suka daina girma, ta kamu da wata cuta da ba a san irin ta ba, wanda yasa ta naƙasa, ba ta iya yin ayyukan yau da kullun kamar tafiya, rarrafe ko ma sarrafa yawancin kayayyaki.

Sai dai ta ci gaba da zama a cikin bokitin roba, jim kadan bayan hoton ya fara yaduwa, wani da ba a bayyana sunan shi ba ya bata kyautar keken guragu don saukaka jigilar ta. Iyayen Rahama sun tabbatar da cewa sun kashe kusan naira miliyan daya wajen nema mata lafiya amma abin ya ci tura.

Rahama ta rasu a ranar 25 ga Disamba, 2016 tana da shekaru 19 a Kano, Najeriya, ta rasu ta bar iyayen ta da ‘yan uwan ta.

Allah ya gafarta mata, ya ta huta….