Tarihin Jarumar Kannywood, Ummi Rahab

Ummi Rahab fitacciyar jaruma ce a yankin arewacin Najeriya. Jarumi Adam A. Zango ne ya horas da ita. Baya ga kasancewar ta jarumar da ta yi fice a masana’antar Kannywood, Ummi ta kasance mai fasahar waka.

Ummi Rahab Jarumar Kannywood ce mai jan hankali, mai tashe. Ummi jaruma mai hazaka ce wacce kawo yanzu ta dauki hankulan masoyan Kannywood da dama.

Ita ma Ummi Rahab tana daya daga cikin matasan jaruman Kannywood da suka nuna haƙiƙanin yadda za su iya ɗaukar masana’antar fina-finai a cikin shekaru kaɗan masu zuwa.

Jarumar ta kuma shahara da fitowar ta a cikin fim din “Ummi Takwara” wanda ya jawo mata shahara.

  • Sunan Gaskiya: Ummi Rahab
  • Ranar Haihuwa: April 7, 2004
  • Garin Haihuwa: Kaduna
  • Ƙasar Haihuwa: Najeriya
  • Sana’a: Fim (Kannywood

Ummi Rahab ta yi aure tare da tauraron hiphop kuma furodusa fina-finan Hausa, Lilin Baba a jihar Kano.