Tarihin Jarumar Kannywood, Momee Gombe
Maimuna Gombe Abubakar wacce aka fi sani da (Momee Gombe), yar wasan Kannywood ce ta Najeriya.
An haifi Momee Gombe a ranar 11 ga watan Yulin 1999 a jihar Gombe ta Najeriya. Ta yi makarantar firamare da sakandare a Gombe. Jarumar dai ta fito tare da mawakin Hausa kuma jarumi Adam A Zango wanda ta bayyana a matsayin jagoranta a masana’antar Kannywood, sai kuma mawaki Hamisu Breaker da wani mawaki kuma jarumi Garzali Miko da sauran matasan mawakan Hausa a Arewacin Najeriya.
Momme Gombe ta auri fitaccen mawakin Hausa Adam Fasaha ne a shekarar 2021, amma ba a yi wata guda ba auren ya ƙare, inda mutane da yawa ke rade-radin cewa dangantakar ta da Hamisu Breaker ce ta haddasa mutuwar auren.
Ta fito a fina-finai sama da 30, daga cikin su akwai:
– Kishin Mata
– Asalin Kauna
– Alaqa (Series)