Tarihin Bello Maitama Yusuf CON, Sardaunan Dutse
Sanata. Alh. Dr. Bello Maitama Yusuf GCON, an haifi Sardaunan Dutse ranar 14 ga Afrilu 1947) ɗan siyasan Najeriya ne, ɗan kasuwa, kuma Sanatan Tarayyar Najeriya.
Ya taba rike mukamin ministan harkokin cikin gida a shekarar 1979 sannan ya rike mukamin ministan kasuwanci a shekarar 1982.
Ya yi karatu a jami’ar North Gate dake Washington, kuma ya kasance memba a rusasshiyar jam’iyyar National Party of Nigeria.
Kafin shiga harkar siyasa, ya kafa kamfanin Quartz Integerated Services Nigeria Limited bayan ya kammala jami’a, shahararren kamfani ne kuma mai matukar tasiri a fannin gine-gine wanda ya fara aiki a Kano.
Bugu da ƙari, shi ne shugaban hukumar gudanarwar wasu kamfanoni huɗu na gine-gine a lokacin, wanda hakan yasa ya zama ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta hamshakan attajirai a duniya.
Baya ga wannan, ya kasance lauya kuma ya taba zama babban magatakarda a kotun Majistare da ke Kano. Ya kuma kasance dan majalisar wakilai, kuma har lokacinsa yana daya daga cikin ‘yan biloniya na Jigawa.
Bello Maitama shi ne ya kafa wa dukkan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa a Nijeriya. A matsayinsa na ministan kasuwanci, ya kasance mai kula da takaita kayayyakin da ake shigowa da su Najeriya wanda ke tabarbare dukiyar kasa ta ketare.
Bello Maitama Yusuf CON ya rasu a 13/10/2023.