Al'umma

Tarihin Bawa Jan Gwarzo, Wane Ne Shi?

Takaitaccen tarihin Bawa Jan Gwarzo.

Bawa Jan Gwarzo wanda asalin sunan shi na gaskiya (Umaru Dogo), shi kaɗai mahaifiyar shi ta haifa, kamar yadda masana suka bayyana kuma yana da ƴan uwa guda goma sha ɗaya, kuma Allah shi ya zaɓa a cikin su domin sarauta a wannan lokaci.

Sunan mahaifin Bawa Jan Gwarzo (Amadu), wanda ake kiran shi da Almada, bayan rasuwar mahaifin Jan Gwarzo ne jama’a daga cikin masu mulki suka nuna cewa sun fi ƙaunar a bai wa BJan Gwarzo sarautar domin ya gaje shi.

Dalilin wannan suna na (Bawa Jan Gwarzo) kuwa shi ne, ya kasance mutum ne mai yawan ibada da roƙon Allah akan ya bashi sarautar da zai zamana yafi ƙarfin duk wani mutum da dabba da ke yankin su.

Shekara goma ya ɗauka ya na ibada, duk ranar juma’a yakan fito ya je masallaci yi sallar Juma’a da shi ya koma ba tare da ya yi hira ko wani dogon zance da kowa ba, bayan ya fito ne daga inda ya ke ibadar (bayan shekara 10) sai Ƙanin shi ya ce lallai Bawa ka zama Jan Gwarzo.

Ana naɗa shi sarauta sai ya kira duk sarakunan ƙasar Hausa da su Nupe da yankin Keffi da Nijar, ya ce da su ” A zo bikin sarautar sa, a wurin naɗin ya ce da su “To daga yau kada a sake yaƙi a tsakanin daula da daula, Hausa ta koma ɗaya ƴan uwan juna ne, don haka babu maganar yaƙi a tsakanin ƴan uwa”.

Jan Gwarzo yana ɗaya daga cikin waɗan da su ka bawa Ɗan fodiyo agaji na wurin zama harma ya kai Ɗansa Yumfa wajen Ɗan Fodiyo don ya yi karatu.0

A tarihin Jan Gwarzo bai taɓa yaƙi da ko wacce daula ba har ya koma ga Allah, saboda shi mutum ne mai ibada da rashin son zubar da jini, kuma sai da ya rasu sannan abubuwa su ka taɓarɓare.

Sau uku ya fita rangadi a rayuwar mulkin shi:

1- Yayi wajen Nijar a rangadi.
2- Bayan wasu shekaru ya ziyarci Ƙasashen Hausa.
3- Sai kuma na ƙarshe inda yayi rangadi wajajen yankin Kwara.

Yayi shekara 82 a duniya, inda yayi mulki na tsawan shekara ashirin da biyu.

Kafin Ɗan fodiyo ya ci Gobir da yaƙi lokacin Muh’d Yunfa sai da yayi shekara bakwai ana gwabza yaƙi sannan aka samu nasara akan sh, bayan da akai masa taran dangi da sojojin ƙasashen da aka ci su da yaƙi na ƙasar Hausa.

Wannan shi ne tarihin Bawa Jan Gwarzo a taƙaice kamar yadda bincike da dama ya nuna.

Allah ne mafi sani.