Al'umma
Tarihi: Ladi Kwali, Matar Da Ke Jikin Naira Ashirin ‘₦20’
Matar da ke kan takardar Naira Ashirin ta Najeriya, ita ce Ladi Kwali, wacce aka haifa a garin Kwali da ke yankin Gwari a Arewacin Najeriya, yankin da ya mamaye sana’ar tukwane.
Ladi Kwali ta kware sosai har ta kai ga shaharar ayyukan hannunta a kasashen Turai da Amurka kuma a karshen shekarun 1950 zuwa farkon 1960, kwazon da ta yi ya samu nasara yayin da aka baje kolin abin da ta yi a Landan a dandalin Berkeley.
Ta kasance fitacciyar mai tukwane a Najeriya, kuma ta sami lambar yabo ta digirin digirgir kuma ta samu MBE a shekarar 1963 duk da cewa ba ta yi karatun boko ba.