Takaitaccen Tarihin Dr. Jabir Sani Maihula
An haifi Dr. Jabir Sani Maihula a garin Sifawa a jihar Sokoto, ya fara karatun addini a wurin mahaifansa, sannan ya shiga makarantar allo da ta islamiyya kafin ya shiga makarantar firamari. Kana, yayi karatun sakandire duk garin sakkwato. Kuma ya fara rike shugabancin dalibai tun yana daga aji biyu na firamare. Ya rike mukamai da suka hada, monita aji, limamin makarantar sakandiri, mataimakin shugaban dalibin, da rikon shugabancin daliban makarantar da yayi.
Sheikh Dr. Jabir Sani Maihula ya fara shahara ne a fanni lamarin addini da neman ilimi, tun yana da shekaru sha biyu, lokacin da yayi fice a cikin wani shirin gidan rediyon jihar Sakkwato, na “Mudali’ar Musulunci” A cikin wannan shirin na kacici-kacici, akan yiwa yara tambayoyi gameda addinin musulunci, kuma Jabir Sani Maihula, ya shahara ne wajen amsa tambayoyin ga duk mai sauraren radio a wannan lokaci.
Bayan kammala karatunsa na sakandire, Jabir da mutum dari uku da sittin sunyi wani kos a jihar Sakkwato wanda jami’ar musulunci ta Madinah ke shiryawa a kowacce shekara awancan lokacin, kuma domin kula da hazaqarsa, kokarinsa da karancin shekarun sa yasa malaman dake koyar da wadannan kosa kosai din ya burgesu, kuma suka jashi ajiki. Bayan anyi jarabawar kammalawa, Jabir ya kasance cikin mutum shida da suka sami nasarar samun gurbin karatu a jami’ar musulunci ta Madinah a shekara ta 1999.
A Madinah, inda Sheikh Jabir yayi shekara shidda yana karatu, yafara ne da fara kwarewa a harshen larabci, daga shekara ta 1999 zuwa 2000. Daga nan sai ya fara karatun digiri dinsa a fannin Hadisi da karancen karancen addinin Musulunci a shekara ta 2000. Bayan kammala digiri da yayi a shekara ta 2004, Sheikh Jabir ya yi wata diploma ta gaba da digiri akan harkokin alkalanci da siyasa a musulunci, a sashen kula da Shari’a a jami’ar musulunci ta Madinah.
A lokacin da yake Madinah, Sheikh Jabir yayi karatu a gaban manya manyan Malamai a Masallacin Annabi (S.A.W), cikin su akwai, Sheikh Abdul Muhsin al-Abbad, wanda yayi karatun Sunani Abi Dawud da Sunani Tirmizi a hannu sa, haka nan ya karanci Umdatul Ahkam da Umdatul Fiqh a wurin baban malamin nan na fiqhu, Sheikh Muhammad Mukhtar al shanqity.
Muwadda a wurin Sheikh Umar Hassan Fullata, da kuma tafsiri a wurin Sheikh Abubakar Ibn Jabir al-Jaza’iri. Haka ma ya halarci karatukan malamai, kamar Sheikh Muhammad Ibn Salih al Uthaimeen, Sheikh Salih al-Fauzan, Sheikh Bakar Abdallah Abu-Zaid, Sheikh Abdalla Mutlaq Sheikh Salih Ali Sheikh, Sheikh Abdul Aziz Ali Sheikh, Sheikh Salih luhaidan, da sauran su
Mai-Hula ya fara harkar da’awa tun yana hidimar ƙasa a Abuja a shekarar 2005, yana koyar da mutane karatu da kuma yin wa’azi a Abuja.
A 2006 ya fara koyar da yaran unguwa a Sakwwato. A 2009 kuma ya fara babban majalisi a Sokoton.
“Daga lokacin abu ya kankama na sa ɗambar karatun Sunani Abu Daudu har yanzu ana yi ba a kammala ba,” in ji shi.
Malam ya ce duk ranakun Alhamis da Juma’a ana karance karance a gidansa.
Ya zama limamin Juma’a sannan akwai masallatan Juma’a uku a Sokoto da ke ƙarƙashinsa.
A 2011 ya samu damar zuwa Birtaniya yin digiri na biyu a Jami’ar East London kan Ilimin Musulunci da na Gabas Ta Tsakiya. Ya koma Najeriya a 2012 inda ya fara aiki a Jami’ar Jihar Sokoto a shekarar 2013.
Ya koma Birtaniya a shekarar 2014 don karatun digirin-dirgir a Jami’ar Nottingham. Ya rike Shugaban Musulmin Jami’ar Nottingham (wato Isoc president) daga Maris 2016 zuwa Maris 2017. Kuma shi ne limami Juma’a na farko na Jami’ar ta Nothingam. Ya zama Shugaban sashen Nazarin Larabci da Addinin Musulunci a Jami’ar Jihar Sokoto daga 2019 zuwa 2023. A yanzu haka an zabeshi Dean Faculty of Arts and Islamic Studies daga Maris 2023.
Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya zabo shi daga cikin majalisar zartarwarsa ta jihar Sokoto, inda ya bashi Kwamishinan lamuran addini, an rantsar da shi a ranar Attanin data gabata a ranar 21 ga watan Augusta 2023.