Tahir M. Fagge Bai Rasu Ba, Yana Nan Raye

Jarumin KannyWood, Tahir M. Fagge bai rasu ba, yana nan a raye.

Idan za’a iya tunawa, ya kwanan an yi ta yada jita-jitar cewa M. Fagge ya rasu a kafafen sada zumunta, musamman Facebook.

Arewa Times Hausa ta yi bincike kan wannan labarin sosai, kuma binciken ya nuna cewa labarin karya ne, kuma ba na gaskiya ne ba, domin baya wata babbar madogara.

Ga abin ake yadawa na karyar rasuwar M. Fagge;

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN 😭

Allah yayiwa Babban jarumin Kannywood ɗin nan mai suna TAHIR M. FAGGE sakamakon Ciwon Zuciya da ya ta Fama dashi kimanin watanni 5 da suka shuɗe.

TAHIR M. FAGGE dai ya rasu ne a yammacin yau Laraba 08/03/2023 A Asibiti.

za’ayi jana’izar shi gobe Alhamis da misalin ƙarfe 10:00am na safe.

Allah ya jiƙaanshi da rahama Sannan muma idan tamu tazo yasa mu cika da Imani Ameeeen

Wannan labarin ba gaskiya ne ba.