Ta’addanci: Bello Turji Kachalla Ya Mutu Ko Yana Raye?

A yan kwanakin mutane da dama sun shiga cikin wasa-wasin cewa ko dan ta’addan nan da yayi kaurin suna wajen kisan gilla, wato Bello Turji Kachalla yana raye ko ya mutu.

Duba da irin rashin imanin dake a zuciyar Bello Turji, wanda kashe mutane manya ko kananan yara bai zama wani aiki a wajen shi ba, mutane sun shiga shakku kasancewar an samu wani lokaci kawo yanzu ba’a ji duriyar dan ta’addan ba, mutane sun fara tambayar shin Bello Turji yana raye ko ya tafi lahira?

A yau zamu amsa wannan tambayar kamar yadda bayanan dake a hannun mu suka tabbatar game da shi wannan dan ta’addan marashi imani, Bello Turji.

Dukkan bayanai da muka tattara sun nuna cewa Bello Turji yana nan a raye, kuma lafiyar shi kalau.

Idan ma ba’a manta kwanakin na Turji ya yiwa Malamin addinin Musulunci, Bello Yabo martani akan wasu malamai da Malmin yayi na cewa Turji ba Musulmin kirki ne ba, kuma baya Sallah.

A wani bayani daban, wasu rahotanni da bamu kai ga tabbatar da ingancin su ba, sun bayyana cewa an hangi Turji cikin wata mota kirar Hilux sabuwa a wani gari mai suna Jangeru cikin Zamfara, in da wasu mayakan shi ke take mai baya da gaba.

Idan kun duba wannan shafin Arewa Times Hausa sosai zaku samu bayanai masu yawa game da Bello Turji.