Tarihin Mallam Ayuba Musa Lukuwa

Mallam Musa Lukuwa, wanda cikakken sunan shi shine; Ayuba Musa Lukuwa, shahararren malamin addinin Musulunci ne dake zaune a jihar Sakkwato dake Arewacin Nigeriya.

Mallam Musa ya karantar da dalibai ilimomin addinin musulunci da dama a cikin Sakkwato da kewayenta, wanda daga cikin daliban Mallam Musa akwai Mallam Murtala Bello Assada.

Mallam Musa Lukuwa, mutum ne wanda yayi kaurin suna a wajen gwamnatin jihar Sakkwato da wadansu sarakuna a jihar, musamman idan azo fannonin da suka shafi addinin musulunci.

Idan dai ba’a manta ba, barkewar cutar Korona Bayiros (COVID-19) ta sanya malamin da hukumomi takun saka musamman saboda wasu dokoki da ka shinfada game da tarurrukan addinin musulunci kamar sallah da wa’azi.