Taƙaitaccen Tarihin Dr. Zakir Naik, Da Dalilin Da Yasa Ya Bar India

Dr. Zakir Abdul-Karim Naik ma’aikacin gidan talabijin ne na Islama kuma mai wa’azi. Malamin addini ne wanda ba balarabe ba ne kuma mai magana da jama’a wanda ya mayar da hankali kan addinin musulunci da kamanta addini.

An haife shi: 18 October 1965 (yana sama da shekaru 56) a duniya, a Mumbai, India.

Matar shi sunan ta: Farhat Naik.

Ƴa’ƴan shi sune: Fariq Zakir NaikRushda NaikZikra Naik.

Daga cikin wuraren da Mallam yayi karatu akwai: K. C CollegeUniversity Of MumbaiTopiwala National Medical College.

Naik, dan shekaru 56 da haifuwa mai wa’azin addinin Islama da hukumomin Indiya ke nema ruwa a jallo bisa zargin shi da laifin karkatar da kudade da kuma tada tarzoma ta hanyar kalaman kiyayya, ya bar Indiya a shekara ta 2016, daga nan kuma ya koma Malaysia mai mafi yawan musulmi, inda aka ba shi izinin zama na dindindin a lokacin da Mahathir ya kasance firayam Minista.

Gwamnatin Indiya na kokarin dawo da shi.