Suleiman Da Haruna: Ƴan Arewa Da Suka Auri Fararen Mata

Yanzu dai ba sabon labari ne ba cewa akwai wasu yan Najeriya dake auren tsallake. Abin da hakan ke nufi shine, sun yi aure a wajen kabilarsu, launin fatarsu ko kuma al’adarsu.

A cikin wannan labarin, zaku ga wasu yan Arewacin Najeriya guda biyu (2) wadanda suka auri manyan mata farare (Turawa.

1. Suleiman Isah. Wannan matashin dan asalin jihar Kano ne. Labarin soyayyar shi ya fara ne daga Instagram, dandalin sada zumunta inda ya hadu da wata farar fata mai suna Janine Ann Reimann.

Bayan wasu watanni da ganawarsa ya daura aure da Janine Ann a gaban wani fitaccen dan siyasar Najeriya mai suna Shehu Sani. Bayan gamawar su, a zahiri sun zama “maganar gari”. A fili, hakan ya faru ne saboda Janine ta girme suleiman tana da shekaru sama da goma sha biyar (15) akan nashi.

Tun lokacin da Suleiman Isah ya auri wannan baturiya ya rika tadawa mutane a shafinsa na Facebook game da wuraren da suke tafiya. Watanni da yawa da suka gabata, an hango ma’auratan a tsibirin Maldives.

2. Haruna Salisu (Chizo, Germany). Haruna Salisu ya fito daga jihar Kaduna kuma fitaccen mawaki ne, dan wasan barkwanci kuma jarumin Kannywood. Ko da yake an haife shi a Kaduna, Haruna Salisu ya zauna a Kano amma a halin yanzu yana zaune tare da Astrid Kemper, wata Bajamushiya farar fata, wadda ya aura tuntuni.

Labarin soyayya tsakanin Haruna da Astrid Kemper ya faro ne bayan sun hadu a wata rangadi a wajen Najeriya. Bayan wasu watanni da haduwarsu, Haruna Salisu ya auri Astrid Kemper a watan Afrilu, 2019 a Chico, Jamus. Jama’a masu karatu, wasu na ganin cewa wadannan matasan arewa sun auri wadannan turawan ne domin a kara musu karfin kudi.