Alaƙa

Soyayyar Rakiya Da Hamisu Breaker: Babban Abinda Ya Kamata Ka Sani

Daga Mu’az Sulaiman Sa’eed

Da fari dai ban so na saka baki na akan maganar nan ba kwata-kwata ba, saboda a waje na, ba kowane batu ne ya ke buƙatar tankawa ba. To amma abubuwa biyu sun ja hankali na ƙwarai da gaske. Abu na farko shi ne tausayin da Rakiya ta ba ni, ta kuma ba wa mutane da yawa bayan kallon hirar su da ta yi da Hadiza Gabon.

Sai abu na biyu, yadda na ga wasu na alaƙanta cewa wannan masoyin ba wani ba ne illa Hamisu Breaker.

Wannan gaɓar ta biyu ta yi daidai da tunani na bayan kammala kallon hirar da muka yi tare tawa masoyiyar da ba mu wahalar da juna ba. Ina gama kallon, nace mata, Allah yasa ba Breaker Rakiya ta ke nufi ba. Ummu Hanan tace anya kuwa?

Mu dawo maganar mu. A ƙarƙashin wannan gaɓa ta biyu ina da abubuwan faɗa dozin guda kamar haka:

  1. Ban yi wannan rubutun domin aibata wani ko bawa wani kariya a cikin su biyun ba. Illa dai kawai na ɗan san wani abu dangane da alaƙar su biyun.
  2. Hamisu maƙobcin mu ne a unguwar Dorayi, domin gida ɗaya ne tsakanin mu da gidansu, don haka tamkar ƙani yake a waje na tun bai kai shekara biyar a duniya ba. Bayan kasancewar shi maƙobcin kuma tamkar ƙani, Hamisu ɗalibi na ne na tsawon shekaru kafin yai nisa a harkar waƙa, domin kuwa har ya fara waka yana koyar karatu a waje na.
  3. Ban san abin da ya fara haɗa Hamisu da Rakiya ba, amma na tabbatar cewa Rakiya ta yiwa, ko kuma tana yi wa Hamisu so maras misaltawa, domin kuwa ta kan zo ta wuni a gidan su tare da mahaifiyar shi, su yi hira, ta taya ta aiki, kuma ta raka ƙanwar sgu Khadija duk inda aka aiketa (kanti, siyo kayan miya da sauransu), duk da kasancewar matsayin ta na tauraruwar fim (ko nace celebrity).
  4. Ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba, duk lokacin da na shiga gidan su Hamisu na sameta (Rakiya) ko suka fito da Khadija ko da shi Hamisu, in har Hamisu zai gaishe ni to sai ta rusuna take gaishe ni. Saboda duk wanda ta fahimci yana da wata ƙima ko influence akan Hamisu tana girmama shi.
  5. Ba ni kaɗai ba, duk waɗanda suke rukunin gidanjenmu sun saba da ganin ta domin a wancan lokacin ɗai-ɗai ne ranakun da bata gidan su Breaker (ko da baya gari).
  6. Tambayar a nan shi ne, shin Hamisu Breaker ya taɓa soyayya da Rakiya?
  7. Ba zan iya amsa tambayar kai tsaye ba, amma tun a wancen lokacin, abin da mafi yawan mu muka fahimta shi ne Rakiya ke neman soyayyar Hamisu Breaker. Kuma ina da dalilai.
  8. Na taɓa tattaunawa da shi a kan alaƙar shi da Rakiya, musamman akan zuwan da ke gidan su na rashin dacewar hakan. A lokacin ya bani amsar cewa tana son shi ne, shi kuma gaskiya bai aminta ba. Ta kan zo gidan har ta tafi ba su haɗu ba, domin ita tana zuwa wajen mahaifiyar shi ne da niyyar kamun ƙafa. Don haka ba yadda zai iya hana ta zuwa, saboda ya faɗa mata bata ji ba. Mun yi makamanciyar wannan maganar da mahaifiyar Hamisu wata rana, kuma amsar da na samu bata ci karo da abin da Hamisu ya faɗa min ba.
  9. Kamar yadda na ji (daga wasu abokansa) cewar akwai waƙoƙin da sukai tare da Hamisu wanda ita ta ɗau nauyin su, ta biya shi, ta kuma roƙe shi su yi video ɗin waƙar tare.
  10. A lokacin da duk waɗannan abubuwan suke faruwa, Hamisu bai yi shura an san shi a ko ina kamar yanzu ba. Don haka in dai ya tabbata shi ne wanda Rakiya ta ba da labari, to tabbas ba ɗaukaka ce ta raba su ba, tun farko ta gino soyayyar ta ne da tubalin toka, ko kuma son maso wani.
  11. Na iya tunawa a cikin hirar ta akwai inda tace “Ya yi min duk wani abu da ya kamata na rabu da shi, na ma manta da shi a rayuwa ta, amma ban rabu da shi ba”. Idan har ya tabbata Breaker ne take nufi, to tabbas ni kai na naga dagiyar ta a irin yadda tun yana kulata, har ya zama yana sha mata ƙanshi, da mu’amalar da za ta rabu da shi ɗin amma bata dena ba.
  12. A taƙaice, ba ina ganin laifin Rakiya ba ne, domin sha’anin so ya fi ga haka. Haka kuma ba ina kare Hamisu ba ne, amma ni ganau ne cewa tun ba a san Hamisu Breaker sosai ba, ya nuna rashin karɓar soyayyar Rakiya, don haka rabuwar su ba ta da alaƙa da matsayin da ya samu a rayuwa.