Soja Ya Bindige Kan Shi Saboda Jin Dadin Mahaifiyar Shi [Darasi]

Wani soja dan kasar Argentina ya buga waya ga a mahaifiyar shi daga barikin shi bayan wani yaki da ake kira yakin Falkland, inda ya tambaye ta ko zai iya dawowa tare da wani soja abokin shi da ya samu rauni, tunda gidan wannan soja yana da nisa, kuma ba zai iya tafiya mai nisa ba, sakamakon yanke mai kafa, kuma ya rasa ganin shi.

Duk da cewa mahaifiyar ta yi matukar farin ciki da dawowar dan ta daya tilo a raye daga yakin, amma ta ki karbar bakuncin abokin shi da ya ji rauni sosai, tana mai cewa ba za ta iya ganin irin wannan bala’in ba.

Dan ta yi shiru, sannan ya kashe wayar, ya harbe kan shi.

Soja dan ta shi ne abin takaici, kuma sojan da aka yanke wa kafa wanda mahaifiyar shi ba ta son gani.

Soja  ba ya son azabtar da mahaifiyar shi har tsawon rayuwar ta, sai ya yanke wannan shawarar, domin sojan ya maganar ya rasa kafa da gani.

An nakalto daga ɗan gajeren labari na marubuci dan Colombia, Gabriel García Márquez