Shugabannin Kasa Biyu Na Mulkin Soja Da Suka Yi Murabus Daga Mulki
A cikin mulkin kama-karya na soja, sojoji suna da cikakken iko ko karfi a kan ikon siyasa, kuma mai mulkin kama-karya babban jami’in soja ne. Irin wannan mulkin kama-karya ana kiran shi mulkin kama-karya na soja. Ga jerin tsoffin shugabannin sojoji da suka yi murabus daga mukaman su.
Ibrahim Babangida
Babangida wanda ke mulkin Najeriya tun bayan da ya hau mulki a juyin mulkin soja a shekarar 1985, ya fuskanci matsin lamba kan ya mika mulki ga gwamnatin dimokradiyya.
Wannan matsin lamba ya yi kamari ne bayan da Babangida ya soke sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yuni da ya kamata ya samar da farar hula.
A watan Agustan shekarar 1993, Janar Babangida ya sauka daga kan karagar mulkin Najeriya sakamakon rikicin da ya barke a ranar 12 ga watan Yuni.
Olusegun Obasanjo
Obasanjo ne ya jagoranci zaben 1979 sannan ya baiwa sabon zababben shugaban farar hula, Shehu Shagari mulki, a wani bangare na kudirinsa na maido da mulkin dimokradiyya a Najeriya.
An rantsar da Shehu Shagari a matsayin shugaban Najeriya na farko kuma shugaban soja a ranar 1 ga Oktoba, 1979. A karon farko a tarihin Najeriya Obasanjo ya mika mulki ga Shagari ba tare da fada ba.