Shin Kun San Waye Abacha Da Gaske?

Da gaske mun san Abacha?

Janar Sani Abacha ya tafiyar da tattalin arzikin Najeriya fiye da kowace gwamnati da aka zaba tun 1979.

Tare da Abacha, al’ummar kasar sun samu nasarorin da ba a taba samu ba a fannin tattalin arziki inda aka samu karin kaso 975 cikin 100 na kudaden ajiyar kasar waje daga dala miliyan 494 a shekarar 1993 zuwa dala biliyan 9.6 a tsakiyar shekarar 1997, da kuma rage bashin da ake bin Najeriya daga dala biliyan 36 a shekarar 1993 zuwa Dala biliyan 27 zuwa 1997.

Abacha ya dakatar da duk wasu tsare-tsare masu cike da ce-ce-ku-ce da magabacinsa, Ibrahim Babangida ya bullo da shi tare da rage hauhawar farashin kayayyaki daga kashi 54% da ya gada zuwa kashi 8.5% a mutuwarsa a shekarar 1998.

Janar din ya kashe makudan kudade fiye da yadda ake kashewa akai-akai inda aka cimma wadannan duka yayin da ake siyar da mai akan dala 15 akan kowacce ganga.

Har yanzu dai ba a yi daidai da cin gajiyar tattalin arzikin Abacha ba har zuwa yau.