Sheikh Guruntum Ya Rabawa Talakawa Marasa Ƙarfi Shinkafa Buhu 1,000

Babban malamin Addinin Muslunci Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum yayi rabon Shinkafa har buhu dubu daya (1,000 bags) jiya a kofar gidansa da yake Bauchi.

Hakika, babu shakka wanann abu ne da ya chancanci jinjina da fatan alkairi, lallai irin wannan aiki ake so, ciyar da gajiyayyu da marayu gagarumin aiki ne a musulunci.

Allah ya sakawa Sheikh da mafificin alkairi yasa aiki ne karbabbe. Muna fatan sauran malamai, attajirai da kowa zai yi koyi da irin wannan aikin na alkairi.