Shawarwari 20 Ga Matan Aure

A wannan zamani mai cike shubuhohi, mata suna cikin zullumi a gidajen auren su saboda yadda auren su yake yawan mutuwa kan yan matsalolin kaɗan.

Da sunan Ubangiji Mai rahama Mai jinkai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi (Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam) da sahabbansa, da dukkan wadanda suka bi tafarkinsu har zuwa ranar tashin Alkiyama.

Bayan haka, shakka babu a wannan zamani da muke ciki ’yan mata da zawarawa masu yawa da matan aure suna cikin dar-dar da tsoro da rashin kwanciyar hankali a gidajen auren su, saboda yadda auren su yake yawan mutuwa, bayan kuma an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakanin ma’auratan.

A kasa ga wasu shawarwari 20 wadanda idan mata suka yi la’akari da su insha Allahu za a samu kyautatuwar zaman aure su cikin nisahadi.

1– Aurenki ya zama domin neman yardar Allah kika yi ba don tara abin duniya ba.

2– Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin aure.

3– Ki zaba wa ’ya’yanki uba ta hanyar auren wanda kika yarda da addininsa da dabi’unsa har ma da dangantakarsa.

4– Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.

5– Kada ki zama mai kaurace wa shimfidar mijinki.

6– Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.

7– Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.

8– Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya iri-iri.

9– Ki zama kwararriya wajen iya girki nau’i-nau’i.

10– Ki zama kin iya barkwanci a magana wajen bai wa mijinki dariya.

11– Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abin da mijinki ya ba ki.

12– Ki rika wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.

13– Ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki da sauransu.

14– Ki rika girmama iyayen mijinki da ’yan uwansa da abokansa.

15– Kada ki zama mai satar kayan mijinki.

16– Kada ki zama mai satar fita zuwa unguwa.

17– Ki guji leke a gidan mijinki, don yana daga cikin abin da yake raba aure a tsakanin Hausawa.

18– Ki rika gode wa mijinki a cikin abin da ya ba ki.

19– Ki kiyaye abin da mijinki ya fi so.

20– Ki kiyaye abin da mijinki ya fi son ci da safe, rana da kuma dare.