Shahararren Malamin Addinin Musulunci, Dr. Ahmad BUK Ya Rasu

Dr Ahmad Bamba, fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Kano ya rasu a yau Juma’a, 7/1/2022.

Malam Abdullahi Ahmad, daya daga cikin ‘ya’yansa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai yau Juma’a a Kano.

Abdullahi yace malamin, wanda aka fi sani da Dr Ahmad BUK, ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano ranar Juma’a, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Bamba dan kasar Ghana ne wanda ya zo Najeriya bayan ya yi karatu a kasar Saudiyya inda ya koyar a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Ya kasance daya daga cikin fitattun malamai wadanda suka kware wajen koyarwa da tafsirin Hadisi, hadisan Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama.

Bamba yana gabatar da laccoci na Hadisi na mako-mako a masallacin BUK na tsawon shekaru, kafin ya koma masallacin kansa mai suna Darul Hadith a Kano.