Saurayina Balarabe Ne Ya Tilasta Ni Saka Hijab Kafin Ya Fita Da Ni – Zee-Zee

Tauraruwar fina-finan Hausa yar Najeriya da ke zaune a Dubai, Ummi Ibrahim Zeezee, ta bayyana a shafin ta na Instagram da aka tabbatar da cewa ta bayyana abin da ya faru tsakanin ta da saurayin ta Balarabe a Dubai.

Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood wadda ke aiki a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a koda yaushe tana sabunta bayanai ga masu bibiyar ta a shafukan sada zumunta game da duk wani shiri nata.

An dai ganta a sabon sakon da ta wallafa a shafin ta na Instagram sanye da hijabi ja da baki.

An jiyo ta tana cewa “yau saurayina Balarabe (baby) ne ya tilasta min na tabbatar na yi ado da Hijabi kafin ya fitar da ni zuwa wani gidan abinci. Wannan ni ne a cikin abaya baki da ja ina ji ba dadi”.

Tauraruwar fina-finan ta shahara da soyayyar sa ga turanci. Tana cikin manyan yan mata a gidan sinimar Hausa da a koda yaushe ke jan hankalin jama’a don kyan gani.