Sai Da Na Biya Wani Mutum Yayi Min Ciki, Saboda Maza Sun Guje Ni Akan Lalura Ta

Wata mata mai suna Jackie mahaifiyar yaro daya ta bayyana yadda ta biya wani mutum kudi domin ya yi mata ciki domin babu wani mutum da ya so ya aure ta saboda nakasa.

A cewar ta, a lokacin da take ‘yar shekara 10 ‘yan daba sun far wa ‘yan uwanta inda suka kashe wasu daga cikin ‘yan uwanta, sannan suka juya wajen ta suka sare mata hannu da ido daya.

Ta ce, a zaton su, ta mutu ne suka tafi, abu na gaba ta tashi a asibiti inda wani bahaushe mai kyau ya ruga da ita aka yi mata magani daga baya aka sallameta ta koma gida, ta zauna da wata makwabciyar ta har ta girma, shekaru kuma ta ji kamar za ta iya zama mai zaman kanta.

Ta ce babu wani namiji da ya taba tambayar ta aure, kuma tunda ta kasance tana son samun iyali da ‘ya’ya sai ta yi tunanin biyan wani namiji ya yi mata ciki, ta sami wani mutum wanda ya yarda ya yi mTa ciki ta biya shi.

Ta ce ta tara kudi ta biya wa wancan mutumin ya yi mata ciki, ta yi sau daya kuma ta samu ciki ta biya shi, kuma daga ranar ba ta kara ganin mutumin ba. Bayan wata tara ta haifi diya mace, ta ce tana jin dadi a duk lokacin da ta ganta kuma tana aiki tukuru don ganin ta samu duk wani abu da take bukata duk da yana da wahala ta yi wani aiki tunda ba ta da hannu.

Yanzu haka Jackie ta roki masu hannu da shuni da su taimaka mata ta yi aikin da zai taimaka mata ta iya kula da danta da kuma iya biyan kudin haya.

Nilimlipa Pesa Mwanaume ili Anipe Mimba|KILICHOFUATA KILINISIKITISHA