Rikici Ya Kaure, Yayin Da Ango Ya Ki Biyan Kudin Turare Dubu Dari 200

Wani mutum mai suna Mubarak Saleh ya bayyana yadda wani aure ya kusa rushewa saboda angon ya ki ba da kudin da dangin amaryar suka nema domin sayen turare.

Ya ce dangin amaryar sun nemi ango naira N200,000 bayan ya biya sadaki kuma ya kai kayan da ake bukata don bikin aure a Maiduguri, jihar Borno.

Angon wanda ya biya sadaki dubu dari N200 da kudin akwatuna dubu dari N800, ya ce zai iya ba su N50,000 ne kawai na turare, idan ba za su karba ba to a dage daurin auren.

Sai dai mahaifin amaryar ya ce bai kamata turare su zama dalilin soke bikin ba don haka ya karbi dubu N50.

Mubarak ya ce; “Wani biki ya kusa fadowa bcos na turare (Turaren wuta). Iyalan amarya sun nemi da aba su turare 200k, bayan sun biya sadaki da (lefe). D ango yace ko dai sun karbi 50k ko kuma a fasa d aurawa, da mahaifin amarya ya karbo 50k ya ce kudin turare ba zai hana d bikin aure ba.