Rasuwar Dr. Ahmad BUK Ta Girgiza Kano Sosai – Ganduje

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana rasuwar Dr. Ahmad Bamba, fitaccen malamin addinin musulunci a matsayin abin bakin ciki.

Ganduje ya bayyana haka ne a cikin sakon ta’aziyyar da babban sakataren yada labaran sa, Mista Abba Anwar ya aike ranar Juma’a a Kano.

“Rasuwar ta riski jihar sosai, ya kasance hazikin malami a lokacin rayuwarsa, mai zurfin hazaka da asali a cikin karantarwarsa na fadin Manzon Allah Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).

“Ya kasance mai ba da kuzarin zaman tare cikin lumana, wanda hanyar koyarwarsa ta kasance da nufin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin kowane bangare da sauran su.

“Wannan babbar asara ce da ke tattare da bakin ciki,” in ji shi.

Gwamna Ganduje ya bukaci malaman addinin Musulunci na jihar da su yi koyi da kyawawan halaye na marigayi Sheikh.

“Ya kafa harsashi mai karfi a kan yadda ake “Da’awa” yana kiran mutane zuwa ga Musulunci, kuma ya bi abin da yake wa’azi.

“Shi mutum ne mai kirki ta kowane hali,” in ji shi.

Gwamnan a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano ya jajantawa iyalan mamacin.

“Ina mika ta’aziyyarmu ga iyalan Sheikh Dr Ahmad Muhammad-Ibrahim.

“Ba iyalen sa kawai, Kano ko Najeriya ba, har ila yau duk al’ummar duniya sun yi asarar wani abu mai daraja,” in ji shi.

Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da alherinsa da Al Jannah Firdausi, ya kuma baiwa iyalai hakurin jure rashin.