Na Caka Mata Wuka Don Kare Kai Na – Dan China Ya Fadi Yadda Ya Kashe Ummi

Dan kasar China da ake zargi da kashe masoyiyar shi a Kano ya bayyana a gaban kotu cewa ya daba mata wuka domin ya kare kan shi.

Frank Geng Quangrong ya shaida wa babbar kotun Kano ranar Alhamis cewa Ummu ta tunkare shi da wuka bayan wata ‘yar rashin fahimta. A cewar shi, ya yi sa’a ya kama wukar don haka ya daba mata wukar.

A yayin da yake bayyana wa kotu irin halin da ta shiga, Frank ya ce ya je gidan ta ne ya mayar da wani kare da ta ba shi, a haka ne ta fara zagi da kiran sunan shi, ita ma ta je falo ta fito da wuka da ta yi yunkurin fada da ita ta soke shi.

Ya ce: “Lokacin da ta yi yunkurin daba min wuka, sai na rike hannun ta na karbo wukar daga hannun ta”.

“A yayin da take kokarin sake mallakar wukar, ta ciji hannu na na hagu da yatsa na. Ta ci gaba da zagi, fada da kiran sunan mahaifiya ta wanda shi ne cin mutunci mafi girma a al’adun Sinawa”.

“A wannan lokacin, har yanzu wukar na hannu na, sai ta yi amfani da hannun ta ta kama al’aura ta tana jan ta. Na ji raɗaɗi kuma dole ne in kare kai na”.

Mista Frank ya kuma kara da cewa ya yi kuka sosai lokacin da ta mutu saboda yana son ta da gaske.