Al'umma

Mutuwar Malaman Kirki Fitina Ce Ga Al’umma

Hakika mutuwar malamai cikin al-ummah fitina ce babba, da wahala wani daga cikin malamai ya mutu a samu wanda zai maye gurbinsa kuma yakaisa baza’a taba samun haka ba cikin al-ummah, saide a samu wanda zai ringa kwatantawa amma de bade yakai wanda aka rasan ba.

Hadisi yatabbata daga Manzon Allah S.A.W yana cewa:

(إنَّ من أشراطِ السَّاعةِ أن يذهبَ العلمُ ويظهرَ الجهلُ ويُشربَ الخمرُ ويَفشُوَ الزِّنا ويَقِلَّ الرِّجالُ وتَكثرَ النِّساءُ حتَّى يكونَ قيِّمَ خمسين امرأةٍ رجلٌ واحدٌ)

Annabi S.A.W yace : “Yana daga cikin Alamomin Tashin Al-kiyama tafiyan ilmi, da bayyanan Jahilci, da shan Giya, da Yawaitan Zinah, da karancin Maza, da Yawaitan Mata, Har sai yakai kimar na miji daya tukun Mata hamsi mata hamsin”.

Wannan hadisin yana nuna cewa a mutuwar malamai alama ce ta kiya ma ta kusa, kuma jahilai su zasu bayyana da sunan malamta su bada fatawowi, ilimi zai tafi ne tahanyat mutuwar malamai har sai anzo lokacikin da za’a samu jahilai sune ta rigar malumta, suma sun bata kuma zasu batar da al-ummah.

Allah madaukakin sarki da yajikan malamanmu da iyayenmu da suka riga mu gidan gaskiya, ya kuma kyautata makwancinsu, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani.

Ameeen.