Al'umma

Mene Ne Dalilin Da Yasa Ƙasar Amurka Ke Tsoron Ƙasar China?

Wane irin martani al’umma zasu mayar idan suka ji an ce “na’urar daga kaya sama zata iya haifar da barazana ga tsaron wata kasa a wannan karni”? Tabbas wasu mutane zasu dauki wannan maganar a matsayin abin dariya babba. Amma kuma, wannan zancen ya fito ne daga bakin wani babban jami’in kula da tashar jiragen ruwa na Los Angeles ta kasar Amurka.

A kwanakin baya ne idan zamu iya tunawa, jami’in ya ce, na’urorin daga kaya sama (Lifter) da kasar China ke samarwa ka iya haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka, don haka kuma, gwamnatin Joe Biden na shirin zuba biliyoyin daloli wajen samar da na’urorin a cikin gida na daga kaya maimakon amfani da na kasar China.

Duk da cewa hakan abin ban dariya ne matuka, amma ana samun zantuka irin wadannan cikin ‘yan shekarun baya bayan nan. Daga shigowa da kayan karafa da goran ruwa da motoci, zuwa daliban da ke karatu a kasar, har ma da tafarnuwa da gajeren shirin bidiyo, tamkar dukkan su na iya “haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka”. Hakika, Amurka ta kusan gigicewa saboda “tsoron kasar China”.

Amma sabo da me Amurka ke wannan tsoron? Idan muka yi nazari, za mu gano cewa, saurin bunkasar kasar China cikin yan shekaru kadan, hakan yasa wasu Amurkawa, da sauran wasu kasashen yamma cikin damuwa da rashin jin dadi ainun. Don haka suke son kafofin yada labaran su su yi ta yaɗa kalamai akan cewa “barazana daga ƙasar China”, tare da shafa wa kasar kashin kaza, bisa ga yadda suke zarginta da dana wa kasashe masu tasowa “tarkon bashi”, ga shi har na’urar daga kaya da China ta samar na iya leken asiri.

Daga karshe, a ganin su, (mahukuntan Amurka) komai na kasar China barazana ce a gare su domin ita China tana yaƙi danniyar da kasashen yamma ke yiwa wasu ƙasashe masu tasowa, musamman kasashen Afrika.

Advertisement