Al'umma

Manyan Kasashe 10 Mafi Yawan Jama’a A Duniya

Don a ce wata ƙasa ita ce ƙasa mafi girma a duniya yana da ɗan matsala. Domin kuwa a yayin da kasa ta fi yawan al’umma, wata kasa kuma ta fi girma a fannin kasa da tattalin arzikin kasa.

Don haka wannan labarin zai mayar da hankali ne kan kasashen duniya da ke da yawan al’umma.

1.) China: Wannan ita ce kasa mafi yawan jama’a a duniya mai yawan mutane miliyan 1,410.9 da kuma fadin kasa murabba’in kilomita 9,562,900.

2.) Indiya: Wannan ita ce ƙasa ta biyu mafi yawan jama’a a duniya mai kimanin mutane miliyan 1,380.0, kuma kimanin kilomita murabba’i 3,287,300 a cikin ƙasa.

3.) Amurka: wannan ita ce kasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya, tana karbar kimanin mutane miliyan 329.5, da kuma fadin kasa murabba’in kilomita 9,831,500.

4.) Indonesiya: wannan ita ce kasa ta hudu mafi yawan jama’a a duniya mai kimanin mutane miliyan 273.5, kuma tana da fadin kasa murabba’in kilomita 1,913,500.

5.) Pakistan: An kima wannan ƙasa a matsayin ƙasa ta biyar mafi yawan jama’a a duniya tare da kusan mutane miliyan 220.9. Kasar tana da fadin kasa kimani kilomita murabba’i 796,100.

6.) Brazil: Wannan kuma na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi yawan jama’a a duniya da ke da ‘yan ƙasa kusan miliyan 212.6. Haka kuma kasar tana da fadin kasa kimani kilomita murabba’i 8,515,800.

7.) Nigeria: Wannan ita ce kasa mafi yawan al’umma a Afirka. Ƙasar da ke yammacin Afirka ita kaɗai za ta iya yin alfahari da mazauna kusan miliyan 206.1, kuma ƙasar tana da babban fili mai girman murabba’in kilomita 923,800.

8.) Bangladesh: Wannan ƙasa kuma tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi yawan jama’a a duniya da ke da ‘yan ƙasa kusan miliyan 164.6. Haka kuma kasar tana da fadin kasa kimani kilomita murabba’i 147,600.

9.) Rasha: Wannan na ɗaya daga cikin manyan ƙasashe a duniya ta fuskar yawan jama’a da kuma ƙasa. Wannan ƙasa za ta iya yin alfahari da mazauna miliyan 144.1 da kuma kusan murabba’in kilomita 17,098,300 dangane da ƙasa.

10.) Mexiko: Wannan kuma na ɗaya daga cikin manyan ƙasashe na duniya ta fuskar yawan al’umma. Tana da yawan jama’a kusan mutane miliyan 128.9, tare da fadin kasa murabba’in kilomita 1,964,400.

Madogara: https://www.worlddata.info/the-largest-countries.php

https://www.worldometers.info/world-population/population-by-country/