Makiyin Kano Da Arewa Ne Wanda Ya Rubuta Wasikar Rusa Sabbin Masarautu

Duk wanda ya rubuta wasikar neman rusa wasu masarautu hudu a Kano tare da dawo da Sanusi Lamido Sanusi makiyin Kano da Arewa ne.

Mai Martaba Aminu Ado Bayero bai yi wa kowa laifi ba, bai taka wata doka ba, ya farfado da martabar fadar Kano, idan an gayyace shi yana halartar taron haddar Alkur’ani, ba ya da bangaranci, ba ya da hannu a ciki, bai yaki da kowa, bai taba furta kalaman da ba a tsare ba game da gwamnati/siyasa, yana daukar nauyin zama uba ga daukacin mazauna Kano.

HRH Aminu Ado Bayero shine cikakken sarki da zai mulki masarautar Kano, yana da dukkan abin da ya kamata wajen wanzar da zaman lafiya da martabar fadar mai dimbin tarihi.

Daya daga cikin manyan nasarorin da Ganduje ya samu ita ce samar da masarautu hudu, yana kawo wadata, kwanciyar hankali da ci gaba a kauyuka da biranen jihar Kano. Kasa da shekaru hudu ku ga yadda Masarautar Bichi ta ci gaba, ku dubi Masarautar Gaya cikin sauri, kun ga yadda Masarautar Karaye da Rano ke bunkasa fiye da yadda kuke tsammani.

Ƙirƙirar ƙarin masarautu huɗu ya kawo haɗin kai musamman ga al’ummomin karkara.

Tsohon sarki Sanusi Lamido Sanusi ya cancanci a tsige shi, ya manta aikin sarki, ya raina gwamna, ya yi izgili, dan bangaranci ne. Ya zabi ya koma siyasa ne kawai saboda Ganduje ya jefar da Kwankwaso. Sanusi bai da ikon zama jagora ko kuma uba ga kowa, tsige shi shine mafi alheri a lokacin domin munanan ayyukansa suna shafar jihar Kano a koda yaushe.

Sanusi Lamido Sanusi ya haifar da rarrabuwar kawuna da rashin hadin kai a Kano, ya kashe biliyoyin Naira daga asusun Masarautar domin jin dadin rayuwarsa, ya yi tafka magudi tare da almubazzaranci da kudaden Masarautar wajen siyan tufafi masu tsada, motoci, balaguro zuwa kasashen waje da kyamarar daukar hoto. Akwai wani rahoto da ke cewa Sanusi ya kashe sama da Naira miliyan N100 a shekara don samun bayanai na intanet kawai, Sanusi ya manta da matsayinsa na Sarki sannan yana kokarin jin dadin rayuwarsa a matsayinsa na shahararriyar jama’a ya manta da cewa shi dattijo ne kuma shugaba duk da shekarunsa ko wayewar Turawa. .

Ba Ganduje ba, hatta Abba da Kwankwaso ba za su iya jure wa abin da Sanusi ya yi wa Ganduje ba idan suna kan kujerar Ganduje. Ban taba zargin Ganduje da tsige Sanusi ba, na dauki laifin Sanusi ne saboda shi ne ya tayar da wannan rikicin, munanan ayyukan shi suka janyo hakan.

Ban damu ba ko gwamnatin Abba ta dawo da Sanusi, amma ina da tabbacin za a sake tsige shi a nan gaba, saboda ba shi da ikon zama shugaba. Girmamawa juna ne.

By: George Udom

Translation: Arewa Times Hausa