Mai Wushirya Ya Roki Hukumar Afuwa, Domin Nauyin Mahaifiyarsa Dake Kansa

Ku yafe min, ni maraya ne, ba ni da kowa sai mahaifiyata, kuma nauyinta a kaina yake, sakon m Mai Wushirya zuwa ga hukumar Hizbah bayan ta bayyana wanda take nema ruwa ajallo.

Mai Wushirya, wanda ya bayyana hakan a wani bidiyo, ya kara da cewa “Ina neman gafarar hukumar Hisbah su duba girman Allah idan har da gaske ne ana nemana to a kira wayata kai tsaye ko a aiko da sammaci wallahi zan kai kaina ga hukumar cikin sauki.

Tun bayan lokacin kamun da aka yi min a farko wallahi ban sake aikata makamancin irin wannann laifin da ake zargin ina aikatawa ba.