Darasin Rayuwa: Labarin Zaki Da Wani Ɗan Ƙaramin Ɓera

Wani karamin ɓera ya tada zaki daga barci. Ran zakin ya ɓaci sosai, har yayi barazanar kashe ɓeran, kuma ya cinye shi.

Amma a lokacin da ɓeran ya ba shi hakuri yana cewa kashe shi ba zai yi masa wani amfani ba saboda ko ya cinye shi (ba zai koshi ba) haka kuma idan zakin ya yafe masa, wata rana beran zai dawo masa da alheri.

Zakin yayi dariya a kan shawarar beran na taimaka masa amma duk da haka ya bar ɗan karamin ɓeran ya tafi abin sa.

Bayan wani lokaci zakin ya cikin tarkon wani mafarauci, ɗan linzamin ƙaramin ɓeran ya lanƙwasa ta cikin igiyoyin kuma ya kuɓutar da zakin.

Darasi: Babu wani aiki na gari da ba a samun lada kuma babu wani mahaluki da yayi karami da ba zai iya taimakon wani ba.