Labarin Wani “Mahaifi Da Yar Shi” Mai Wayo (Darasi)
Wani mutum ya yanka wata babbar saniya, ya kunna gasa, ya ce wa ‘yarsa: “Ya ‘ya ta, ki kira ‘yan’uwan mu, abokan mu, da makwabta su ci abinci tare da mu, mu ji dadi!
Diyarsa mai wayo ta hau titi ta fara ihu: “Don Allah a taimaka mana mu kashe gobara a gidan Babana!”.
Bayan wasu ƴan tsirarun sun fito da jin ihun ta, sauran suka yi kamar ba su ji kukan ta ba.
Wadanda suka zo, suka ci suka sha, har dare. Baban cikin kaduwa ya juya ga diyarsa ya ce mata:
“Mutanen da suka zo da kyar in na san su, wasu kuma ban taba ganin su ba. To, ina dangin mu, abokan mu, da maƙwabtan mu?”.
‘Yar ta amsa wa mahaifinta cewa: “Wadanda suka fito daga gidajen su sun zo ne don su taimaka mana wajen kashe wuta a gidan mu, ba don bikin ba. Wadannan su ne suka cancanci karamci da alheri”.
Mutanen da kake tunanin naka ne ba su taba zama naka ba. Wannan shi ne baƙin cikin rayuwar da muke rayuwa ciki a yau.