Labarin Ban Dariya Na Wasu Malaman Coci Uku

Wata rana wadaasu malaman coci (Pastors) su uku (3) suka zauna suka tatauna akan cewa kowane daya daga cikin su ukun zai fito fili ya bayyana ababen da suke damun shi a boye, sai su tattauna a tsakanin su cikin sirri ba tare da daya daga cikinsu ya tona musu asiri ba.

Bayan kowa ya aminta da bayyana sirrin na shi, sai mai magana na farko ya mike yace, “Ni babban abinda ke damu shine; son kudi, domin har son kudi na ya ga kai ina sace wani kaso daga kudin da membobin cocina suke tarawa ba tare da sun sani ba, saboda haka ku tayani da addu’a Ubangiji ya dauke min min wannan dabi’ar.”

Bayan da na farkon ya kammala zancen shi, sai mai magana na biyu daga cikin su yace; “Ni damuwa ta son mata. Domin har tsananin son mata ya kai ga idan naga mace sai nayi duk yadda zanyi domin ganin na kusance ta. A takaice dai kusan duk matan dake zuwa coci na na kusance su. Ina rokon ku da taimaka min da addu’a Ubangiji ya shirye ni.”

Tashin na uku, kuma na karshen su, sai fushe da kuka. Da kyar ragowar malaman cocin biyu suka bashi hakuri yayi shiru.

Da ragowar biyun suka tambaye ya basu nashi labari matsalar sa, sai ya sake fashewa da kuka karo na buyu.

Ana hakan can dai akayi sa’a ya fara magana, sai yace; “Ni damuwa ta shine tsananin munafurci, domin da zarar na bar wurin nan sai kowa yaji abinda dukkan mu muka fada. Ina rokon ku da ku taya ni da addu’a.”

Tambaya gare ku masu karatu, alal misali Idan da kai a cikin wadancan biyun da suka fara magana ya zaka yi?