Kullum Sai Miji Na Ya Duba Al’aura Ta Idan Na Dawo Daga Aiki

Matar wani magidanci mai shekaru 42 a birnin Lusaka na kasar Zambia, ta raba auren ta da mijin na ta saboda kullum idan ta dawo da ga aiki, sai ya duba al’aurar ta, bisa dalilin cewa makwabta sun gaya masa cewa ta na fita yawo da wani dan kasuwa.

A cewar jaridar Zambia Observer, matar, Bessie Msisika Chirwa, mai shekaru 39, ma’aikaciyar jinya a asibiti, ta kai Amos Chirwa, malamin makaranta, kotun Lusaka Boma, bisa dalilin cewa ya na duba al’aurar ta a duk lokacin da ta dawo gida daga aiki, musamman da safe bayan ta yi aikin dare a wannan rana.

Su biyun sun haifi ‘ya’ya biyar tare bayan sun yi aure shekara 13 da wata 10 da suka gabata.

An umurci Amos ya biya kudin kasar kimanin K600 duk wata don abinci da tufafin ’ya’yan su 5 bayan an raba auren.

Amos ya yi kuka sosai a wajen kotu domin ba ya son ya rabu da kyakkyawar matar sa wadda ya ce ya na matuƙar ƙaunar ta.

TRIBUNE…