Al'umma
Kuka: Itaciyar Rayuwa
Itacen kuka itace gama gari a arewacin Najeriya. Musamman a jihar Borno, ana yiwa wata karamar hukuma sunan bishiyar kuka ( karamar hukumar Kukawa).
A yaren Kanuri, ana kiran ta Kuwa, a Hausa kuwa ana kiranta Kuka.
Itacen kuka yana ba da fa’idodi iri-iri, waɗanda suka haɗa da abinci, magunguna, da matsuguni.