Al'umma
Kudin Hayar Gidaje A Abuja Sun Yi Tashin Gwaurayen Zabi
Mazauna babban birnin tarayya, FCT, Abuja, Najeriya basu da wani abin dogaro kan tsadar hayar gidaje da ke babban birnin kasar.
Hakan na faruwa ne yayin da wasu masu gidaje a babban birnin kasar suka dora alhakin tsadar kayan gini a kan lamarin.
Wasu masu gidaje sun koka da cewa yayin da kudin gina sabon gini a Abuja ya haura sama da kashi 200 idan aka kwatanta da yadda yake a da a watannin baya, kula da tsofaffin gidajen kuma ba karamin aiki ba ne.
A cewarsu, kayayyakin da ake amfani da su wajen gine-gine, da rayawa, da gyaran gine-gine basu da araha a Najeriya.
Ginin yana tafiya ne ta hanyar kulawa a tsawon rayuwarsa kuma wasu masu gidaje sun ce ba aiki mai sauƙi ba ne.