Al'umma

Kotu Ta Umarci Wani Mutum A Kano Da Ya Yanka Zakaran Shi Akan Damun Maƙwabta

Wata kotun majistare da ke Kano ta umurci wani Isyaku Shu’aibu da ya mallaki zakara da ya yi kaurin suna da babbar murya da ya yanka shi.

Makwabtan masu shigar da kara biyu ne suka shigar da kara gaban kotun inda suka ce kukan da zakara ke yi na hana su barci da kwanciyar hankali a unguwar.

A wani hukunci da kotu ta yanke a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu, mai shari’a Halima Wali ya ba Shu’aibu umarnin yanka zakaran a ranar Juma’a, 7 ga Afrilu, 2023.