Kana TikTok, Facebook Ko WhatsApp? Karanta Wannan

TikTok, Facebook, X, da WhatsApp sun jami’a!

Yana daga cikin tsari mutane masu hankali idan suka ga abu a SOCIAL MEDIA yana TRENDING suyi bincike sosai kafun suce wani abu akai. Saboda suyi ADALCI, kuma kar su kara yada KARYA da BARNA. Don yanzu 90% na abubuwan da muke gani a SOCIAL MEDIA ba gaskiya ba ne.

Binciken wani

Gaskiya ban san wannan YARINYA mai suna RAHMA SAI’DU ba, sanda wannan abunda yafaru na kora da SCHOOL din da take KARATU suka MATA, kafun nan nama san ta.

Naje kan ACCOUNT nata na TIKTOK, na duba ACTIVITIES nata a TIKTOK. Daga farko ma na dauka nasu ce, saboda irin yarda take fitowa PUBLIC TSIRARA, sai da na tambaya aka ce mun tamu ce.

Dana koma nayi bincike ta bangaran SCHOOL dinta kuma, sai na gano an KORETA ne saboda ta fadi JARRABAWA, bawai don ita TIKTOKER bace yarda wasu suke ta yadawa a SOCIAL MEDIA.

VIDEO da tayi tana KUKA, duk MUNAFURCI ne da neman PUBLIC ATTENTION, don aji tausayinta, amma ba gaskiya take fada ba akan cewa an koreta ne akan ACTIVITIES dinta akan TIKTOK.

SCHOOL din da kansu sun fito sun karyata hakan, cewa JARRABAWA ce bata ci ba kuma bata son zuwa MAKARANTA. Dama ta yaya zakayi tsammanin kokari ga wanda hawa TIKTOK yafi zuwa SCHOOL dinsa yawa.

Ta yaya dalibar HEALTH ace bata zuwa MAKARANTA, kun ga akwai matsala. Wacce zata kula da rayukar AL’UMMAH tana DABI’U irin haka, na kin zuwa MAKARANTA.

Ko da sau daya banji tausayinta ba, saboda ta cancanci korar, saboda ka’ida ne idan kayi fashi sau uku ba tare da dalili mai karfi ba a koreka. Amma ita sai ta jima bata zuwa, amma kullum tana shashewa a TIKTOK.

Ba dai-dai bane, mutum ya kafe CAMERA yazo gaban RING LIGHT da katon HIJAB yana rusa KUKA na MUNAFURCI, yana cewa an zalunce sa, shikenan sai mu yarda ba tare da bincike ba, munga MURJA ma.

Don haka kira da zanyi ma ‘yan SOCIAL MEDIA a guji yada KARYA, kuma duk abunda kaga yana TRENDING a SOCIAL MEDIA ya kamata ayi bincike kafun ace za’ayi sharhi har a yada.

An kwafo.