Kamar Ya San Zai Mutu – Mahaifiya Ta Bayyana Abinda Danta Ya Fada Mata Kafin Ya Rasu

Wata mata wadda ita ce mahaifiyar marigayin Sule ta nuna bacin ran ta game da rasuwar dan ta, inda ta ce kwana uku kafin rasuwar shi ya yi magana da ita kamar ya san abin da zai same shi.

Malama Binta Muhammad wanda ta kadu matuka game da abin da watakila za a iya bayyana shi a matsayin wani lamari mai ban mamaki, ta bayyana cewa dan ta ya aike mata da sako ta mikawa sauran ‘yan uwan shi a lokacin da ta yi magana da shi ta karshe a waya.

Matar da ta yi magana, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito Pidgin ta lura cewa, ba ta zama gari daya da dan ta ba, kuma a ranar da ta yi magana da shi, ya ce mata ta rika gai da duk ‘yan uwan shi maza da mata, kamar yadda ya yi, shine na farko a cikin ‘ya’ya 9 da ta haifa.

Mahaifiyar ta lura da cewa nan take ya mika mata sakon, Sule ya gama wayar, kuma ta yi mamakin jin cewa dan ta tare da matar shi ya mutu a cikin dakin su, bayan sun kunna gawayi a cikin gidan su don ajiyewa suji dumi ga harmattan.

Rahotanni sun ce mutane sun gano gawar Suleiman mai shekaru 28 da ya yi aure watanni 10 da suka gabata tare da matar shi ‘yar shekara 20 a dakin su da ke kauyen Kwa da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano.

Credit Source: BBC News Pidgin