Kaƙiƙanin Abinda Mace Ke Nufi Idan Ta Ce “Ƙyale Ni Kawai” A Wasu Lokuta
Mata wasu halittu ne masu sarkakiya, ya kamata ka kasance mai hankali da kuma lura da yanayin su da halayen su, a matsayin ka na namiji kana bukatar ka fahimci yadda mace ke bayyana ra’ayin ta.
Mace za ta iya cewa wani abu duk da haka tana nufin wani abu daban kuma, tana iya cewa E amma a zahiri tana nufin A’a, ta kuma iya cewa A’A kuma a wata fassarar tana nufin E, ta dauka cewa kai a matsayin ka na namiji ya kamata ka fahimci ainihin ma’ana na abin da take fada kuma idan ba ku yi ba, a ko da yaushe za a sami al’amuran da ke tasowa a tsakanin ku biyu.
Duk yadda ka yi, ba za ka taba fahimtar mace ba amma kana bukatar ka koyi fahimtar cewa abin da suke fada ba shi ne ainihin abin da suke so ba a wani lokaci, musamman cin zafin rai, mafi yawan lokuta mace tana son sabanin abin da ta fada.
Misali, idan ta ce ka rabu da ita, a fakaice ta ce ka bi ta, za ta iya cewa ba ta son magana da kai, amma a fassara, ba ta son a daina zancen, don haka kar ka bari. Kada ka yi kuskuren barin maganar don kawai tace ba ta so.
A matsayin ka na namiji, idan kana son samun kwanciyar hankali kana buƙatar fahimtar harsuna daban-daban da mata suke magana da kuma fassarar su daban-daban. Kuna buƙatar fahimtar yanayin su, kuna buƙatar fahimtar alamun su da motsin su tare da fassarar shi.
Mata kamar jami’a ne da ba za ka taba kammala karatu ba, kawai idan ka yi tunanin ka fahimce su, sai su fito da sabbin kwasa-kwasai da sabbin kalmomi, idan ka yanke shawarar cigaba da karatu, yana da kyau a gare ka, kuma idan ka yanke shawarar kin cigaba to samako mara daɗi.
Babu wani abu da mace ke so kamar namiji mai fahimtar dukkan yaren ta, yana nufin duniya a gare su, idan kana so ka faranta wa matar ka rai, ka fahimci harshen ta, shi ne mabuɗin.