Juyin Mulki A Gabon

Sojoji sun yi juyin mulki a Gabon, sa’o’i kadan bayan da aka ayyana shugaban kasar na shekaru 16 a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a makon jiya.

Shugaba Ali Bongo Ondimba wani bangare ne na daular iyali — mahaifinsa, Albert-Bernard (daga baya Omar) Bongo, ya yi shugaban kasa na tsawon shekaru 41 kafin dansa ya karbi mulki.

Yanzu haka dai Ali Bongo Ondimba yana tsare a gida, inda ake zarginsa da yin magudi a zaben da kuma cin gajiyar arzikin kasa mai arzikin ma’adinai ba bisa ka’ida ba. Juyin mulkin na zuwa ne wata guda bayan da shugabannin sojoji a Nijar suka karbe mulki